Litinin 31 Agusta 2026 - 20:43
Haɗin Kan Musulmi Shi Zai Dawo Musu Da Izzarsu

Hauza/ Abuja: Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), ya jaddada muhimmancin haɗin kan al’ummar Musulmi, yana mai cewa haɗin kai shi ne hanyar dawo da izza da ƙarfin Musulmi.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, ranar Lahadi, 17 ga Rabi’ul Awwal 1448, Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gabatar da jawabin Mauludin Manzon Allah (S) tare da rufe taron Makon Haɗin Kan Musulmi da aka gudanar a Abuja, wanda ya samu halartar ɗimbin mahalarta daga sassa daban-daban na al’ummar Musulmi.

Da yake magana kan kyawawan ɗabi’un Manzon Rahama (S), Jagora (H) ya bayyana cewa Manzon Allah (S) ya yi galaba a kan maƙiyansa ta hanyar kyawawan ɗabi’u, musamman afuwa, tausayi, rahama da yafiya, har ma ga waɗanda suka cutar da shi.

Ya ce ya kamata Manzon Allah (S) ya kasance ramzi da ma’auni ga al’ummar Musulmi wajen kyautata ɗabi’u da mu’amala da juna.

A wani ɓangare na jawabinsa, Jagora (H) ya jaddada cewa rarrabuwar kan Musulmi na daga cikin manyan abubuwan da suka haifar da rauni da koma baya a tsakanin al’ummar Musulmi.

Ya yi kira ga Musulmi da su haɗa kansu tare da dunƙulewa wuri guda domin kare maslahar Musulunci, yana mai cewa haɗin kan Musulmi zai taimaka wajen dawo da izzarsu da ƙarfin da suka rasa.

A cewarsa, wannan haɗin kai ba abin da maƙiyan Musulunci suke so ba ne, domin rarrabuwar Musulmi ita ce ke ba su damar cimma manufofinsu.

A ƙarshe, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya bayyana fatan cewa halin da al’ummar Musulmi ke ciki a yau ba zai dawwama ba, yana mai cewa lokaci zai zo da addini zai ƙara samun kafuwa da ƙarfi, sannan izza da ƙarfin al’ummar Musulmi za su dawo, da yardar Allah.

An gudanar da wannan taro ne a Abuja a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen Makon Haɗin Kan Musulmi, tare da tunawa da zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah Muhammad (S) da Imam Ja’afar Sadik (AS).

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha